
Wata budurwa mai suna Fatima daga unguwar Jiddari Polo a Maiduguri tana karɓar magani a Asibitin Koyarwa bayan da aka ce matar babanta ta zuba mata ruwan zafi, in ji wani mazaunin yankin ranar Laraba.
Rahotanni sun nuna cewa an shirya aurenta cikin watanni hudu masu zuwa kafin wannan mummunan lamari ya faru.
Mazaunin yankin ya bayyana cewa an kama wacce ake zargi, kuma tana hannun ’yan sanda yanzu haka.
Ya kuma roƙi hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su shiga cikin lamarin domin tabbatar da adalci ga wacce abin ya shafa.
’Yan uwa da maƙwabta sun bayyana faruwar lamarin a matsayin babban tashin hankali, suna kuma kiran gwamnati da shugabannin al’umma da su kula da lafiyar yarinyar tare da tabbatar da cewa an hukunta masu laifi.
Yarinyar tana cigaba da samun kulawar likitoci yayin da binciken ’yan sanda ke ci gaba.