Zulum Zai Kaddamar da Ilimin Fasaha da Sana’o’i Ga Daliban Almajirai a Borno

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya umarci Ma’aikatar Ilimi da ta kawo ilimin fasaha da sana’o’i a makarantun Sangaya domin amfanin ɗaliban Almajirai a duk faɗin jihar.

Zulum ya bayar da wannan umarni ne ranar Litinin a Maiduguri yayin karɓar rahoton gyaran fannin ilimin fasaha da sana’o’i a Borno.

Gwamnan ya ce manufar ita ce bayar da damar koyon ƙwarewar zamani ga ɗaliban Almajirai domin su samu shiri don samun aikin yi a nan gaba, tare da ilimin addininsu.

“Ina farin cikin ganin Sakataran Hukumar Ilimin Sangaya yana nan. Na umarci kwamishinan ilimi ya yi aiki tare da ku domin nazarin kawo ilimin fasaha da sana’o’i a makarantun Sangaya namu,” in ji Zulum.

Ya bayyana cewa horar da ‘ya’yan Almajirai da ƙwarewar sana’a ba zai taimaka wajen rufe gibin da ke tsakanin ilimi da buƙatun masana’antu kawai ba, har ma zai rage talauci da rashin aikin yi tsakanin matasa.

Zulum ya ƙara da cewa an kafa kwamitin gyara ilimin fasaha da sana’o’i a jihar, inda yake jaddada cewa babban tsari shi ne tabbatar da cewa waɗanda suka kammala makarantun addini da na zamani suna da ƙwarewar da za su iya neman aiki da ita.

A baya, Shugaban Kwamitin, Alhaji Goni Ibrahim, ya ce an gudanar da nazarin ne ta hanyar ziyarar wurare, tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma kwatancen wasu tsare-tsare, inda aka tsara shawarwari masu dacewa da bukatun ci gaban Borno.

Gwamnan ya kuma yaba da jagorancin kwamishinan ilimi, kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, Injiniya Lawan Abba Wakilbe, kan rawar da ya taka wajen inganta sauye-sauyen fannin.